Isa ga babban shafi

Celine Dion ta soke shagulgula daga 2023-2024 saboda rashin lafiya

Shahararriyar mawakiyar nan Celine Dion ta soke dukkan n shirye-shiryenta da aka shirya gudanarwa a shekarar 2023-2024, tana mai cewa ba ta da karfin yin yawon shakatawa yayin da take fama da wata cuta da ta shafi kwakwalwa.

Fitacciyar mawakiya Celine Dion kenan.
Fitacciyar mawakiya Celine Dion kenan. © WireImage - Brian Rasic
Talla

'Yar kasar Canada mai shekaru 55 a duniya ta bayyana a bara cewa yanayin da take ciki na cutar yana shafar ayyukanta.

"Ina mai bakin cikin sanar da ku halin da nake ciki… ko da yake nima yana karya mini zuciyata, zai fi kyau mu soke komai har sai na shirya dawowa kan aiki, amma duk da haka b azan saraya ba" in ji sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

A cikin watan Disamban 2022, ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram, tana mai bayyana cewa ta kamu da wat acuta da ta shafin kwakwalwa, don haka ba za ta iya rangadin da ta shirya zuwa Turai a watan Fabrairu kamar yadda aka tsara ba.

Sokewar za ta shafi rangadin da za ta yi a kasashe 16 na Turai wanda zata fara a Amsterdam a watan Agusta da kuma kammala kwanaki biyu a filin wasa na O2 da ke Landan a watan Afrilun shekara mai zuwa.

An haifi Dion a Quebec, a kasar Canada kuma ta fara waka tana da shekaru 12, wato lokacin da mahaifiyarta ta aika da nadaddiyar wakar da ta yi ga Angelil, wanda ya ba da jinginar gidansa don ba da kudin kaddamar da wakar ta.

Ta fara rera waka a cikin Faransanci, amma ta fara yin waka da harshen Ingilishi bayan daukar darussan turanci a shekarun 1980.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.