Isa ga babban shafi

Jiragen saman Nijar sun daina dibar fasinjojin Faransa

Wasu majiyoyi daga kamfanonin jiragen saman Jamhuriyar Nijar sun ce, ba za a sake barin Faransawa su hau jirgi su shiga cikin kasar ba. Wannan kuwa ya biyo bayan takaddamar da ke kara ruruwa tsakanin Nijar din da Faransa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar da ta gabata.

Harabar filin jiragen sama na birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar
Harabar filin jiragen sama na birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar AFP - -
Talla

A cewar hukumomin Nijar, duk wani fasinja dan kasar Faransa ya haramta a gare shi shiga cikin kasar.

Shi ma kamfanin jirgin sama na Royal Air Maroc, ya yanke shawarar bin sahun kamfanin Air Burkina wajen dabbaka sabuwar dokar da ta haramta wa Faransawa shiga kasar, matukar ba aiki ne na musamman a hukumance ba.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP da ya tuntubi kamfanonin jiragen saman kasar da suka hada da Ethiopian Airlines da Air Tunisie da kuma Turkish Airlines, kan ko sun yi na’am da sabuwar dokar ko a’a, amma ba su magantu ba.

Yanzu haka, Faransawa da dama ne aka hana su shiga kasar duk kuwa da tuni sun isa filin jirgin saman birnin Yamai na kasar Nijar.

Dangantaka tsakanin Faransa da Nijar na kara sukurkurcewa ne tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokaradiyyar kasar karkashin jagorancin hambararren shugaba Mohammed Bazoum, a ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.