Isa ga babban shafi

Jiragen saman agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun koma zirga-zirgar a Nijar

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen agajin jin kai a jamhuriyar Nijar a ranar Laraba, wanda aka dakatar tun bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a watan Yuli a kasar da sama da mutane miliyan hudu ke bukatar agaji.

Jirgin saman agaji na Majalisar Dinkin Duniya
Jirgin saman agaji na Majalisar Dinkin Duniya AP - NASSER NASSER
Talla

Hukumar kula da jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a Yamai babban birnin kasar Nijar cewa, hukumar kula da jiragen sama ta Majalisar ta dawo da zirga-zirgar jiragen saman cikin gida daga ranar Laraba, bayan da gwamnatin mulkin sojin kasar ta dage haramcin da ta yi.

Juyin mulki

Ofishin OCHA da ke Geneva da yammacin Talata ya bayyana cewa, gwamnatin mulkin sojin kasar ce ta amince jirage su fara zirga-zirga a cikin gida, wanda suka haramta  bayan juyin Mulki da suka yi wajen hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, za ta ba da damar kai kusan tan 2.4 na kayayyakin jinya a kowane wata, da kuma kwashe majinyata da ma’aikatan jin kai.

Jiragen na Majalisar Dinkin Duniya za su kai kayayyaki zuwa manyan yankuna kasar masu nisa, kamar Diffa da ke kudu maso gabas, inda dubban 'yan gudun hijirar Najeriya da 'yan Nijar suka tsere don gujewa tashin hankalin na kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Takunkumin ECOWAS

Jamhuriyar Nijar na fama da takunkuman karya tattalin arziki daga kungiyar ECOWAS tun bayan hambarar da zababben shugabanta na dimokradiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.