Isa ga babban shafi

Chadi ta amince da ratsawar Sojin Faransa ta cikin kasar a hanyarsu ta zuwa gida

Gwamnatin Chadi ta amince da raka ayarin dakarun Sojin Faransa wadanda sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar suka kora, dakarun da za su ratsa ta cikin kasar akan hanyarsu ta komawa gida, a wani yanayi da ake fargabar makomar tsaro a yankin na Sahel bayan ficewar dakarun daga kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar dukkaninsu wadanda ke fama da hare-haren 'yan ta'adda.

Dakarun Sojin Faransa da ke ficewa daga Nijar.
Dakarun Sojin Faransa da ke ficewa daga Nijar. © THOMAS COEX / AFP
Talla

Dakarun Faransar da gwamnatin sojin Nijar ta kora sun kwashi gaba daya kayakin aikinsu, a tafiyar da suke ta kasa mai nisan kilomita sama da dubu 3, inda za su ratsa ta Chadi da jamhuriyar Kamaru, wasu daga cikin hanyoyin da suka kasance mabuyar kungiyoyin mayakan jihadi. 

Cikin sanarwar da babban hafsan tsaron Chadi Abakar Abdelkerim Daou ya fitar a jiya Alhamis, ya ce gwamnatin Chadi ta amince sojojin Faransar su ratsa ta kasar, haka zalika ta kuma amince dakarunta su yi wa na Faransar rakiya daga kan iyakar Nijar zuwa birnin Ndjamena, daga bisani su nufi filin sauka da tashin jiragen saman kasar, haka ma daga kan iyakar Kamaru zuwa filin sauka da tashin jiragen saman kasar da ke birnin Douala. 

A Talatar da ta gabata ne ayarin farko na sojojin Faransa da ke da sansaninsu a Ouallam suka fara ficewa daga Nijar zuwa Chadi da ke makwabtaka da ita, cikin motocin sulke a tafiya mai nisan sama da kilomita dubu daya da 600. 

Wani tsohon kwararre a fannin sufurin sojin Faransa da ke Afrika da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce daga N’Djamena za a kwashe dakarun da kayakinsu na yaki masu hadari ta jirgin sama zuwa Faransa, kazalika za a kuma kwashi sauran sojojin ta teku. 

Akalla sojoji Faransa dubu 1,400 da tarin kayakin yaki aka jibge a jamhuriyar Nijar domin yaki da mayakan da ke da alaka da kungiyoyin IS da na Al-Qaeda, wadanda ke kaddamar da hare-haren ta'addanci a yankin Sahel. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.