Isa ga babban shafi

Amurka ta jaddada goyon baya ga hambararren shugaban Nijar Bazoum Mohammed

Amurka ta sanar da cikakken goyon baya ga zababbiyar gwamnatin farar hula karkashin mulkin demokradiyya a Nijar ta na mai cewa komawar kasar karkashin mulkin farar hula ne zai bayar da tabbacin ci gaban hadaka tsakanin kasashen biyu ta fannin tsaro da ci gaba. 

Shugaba Bazoum Mohammed.
Shugaba Bazoum Mohammed. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sakataren harkokin wajen kasar Anthony Blinken ya tabbatar da hakan ga hambarraren shugaban Nijar Bazoum Mohamed, yayin wata doguwar tattaunawa tsakaninsu.

Amurka Antony Blinken wanda ya zanta da hambararren shugaban na Nijar Mohamed Bazoum ta wayar tarho, ya tabbatar masa da cikakken goyon bayan Amurka gare shi da fatan ganin Nijar ta koma turbar demokradiyya. 

Blinken ya shaidawa Bazoum cewa mulkin farar hula ne kadai zai tabbatar da cikakken kawancen tsaro da na ci gaban da ke tsakanin Nijar da Amurka. 

Tun bayan hambarar da gwamnatinsa da Sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata, har zuwa yanzu sojojin da ke mulki a kasar ta yammacin Afrika na ci gaba da tsare Bazoum. 

Sai dai cikin sanarwar, Amurka ta bukaci gaggauta sakin Bazaoum Mohamed, tare da fatan ganin kasar ta Nijar ta koma turbar demokradiyya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.