Isa ga babban shafi

Ba za mu yi hulda da sojojin Nijar ba - Faransa

A daidai lokacin da aka fara aikin tattara dakarun Faransa a birnin Yamai domin fara janye su daga Jamhuriyar Nijar, Ministar Hakokin Wajen kasar Catherine Colonna, ta ce sam ba za su yin wata hulda da sojojin da suka kwaci mulki a kasar ba. 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da wani sojan kasar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da wani sojan kasar. REUTERS - PASCAL ROSSIGNOL
Talla

Ministar, wadda ke amsa tambayoyi daga wani Kwamiti na Majalisar Dokoki a birnin Paris, ta ce tabbas dakarun za su fice kamar yadda aka tsara. 

A game da janye dakarunmu, ya kamata a fahinci cewa ba za su iya gudanar da aikin da ya kai su a kasar ba tun ranar 26 ga watan Yuli, don haka ba za mu iya yin huldar aikin soji da wadanda suka kwaci mulki da karfi ba, ya zama wajibi su bai wa tsarin dimokuradiyya damar gudana a kasar. Inji Colonna.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar bayaninta.

Ministar ta kara da cewa, "dakarunmu dubu daya da 500 ba za su iya aiki ba a wannan yanayi, aikin fada da ta’addanci bai zai yiwu ba sai an sake bita don samar da sabon salo a tsakanin kasashen Turai da sauran wadanda ke da hannu a wannan yaki da ake yi a Nijar, ciki har da Amurka."

Minista Catherine Colonna, ta ce yanzu haka Tarayyar Turai na shirin lafta wa Nijar wasu sabbin takunkumai kafin karshen wannan wata na Oktoba. 

A yau Alhamis, dakarun Faransa ke fara aikin janyewa daga Jamhuriyar Nijar, kamar dai yadda shugaba Emmanuel Macron ya alkawarta a ranar 24 ga watan Satumbar da ya gabata. 

Sojojin Faransa na farko da suka fara ficewa a yau su ne dakaru 400 da ke a yankin Walam, daf da iyakar Nijar da Mali, kuma sun kasance suna aikin samar da tsaro ne karkashin wani shiri da aka yi wa take Operation Almahaou, wanda babbar manufarsa ita ce samar da tsaro a yankin Liptako. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.