Isa ga babban shafi

Nijar ta umarci sojojinta da su zauna a cikin shirin ko-ta-kwana

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar sun bukaci dakarun kasar da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana domin tinkarar duk wani hari da ake iya kai musu daga kasashen ketare sakamakon karuwar barazanar da kasar ke fuskanta. 

Sojojin Jamhuriyar Nijar yayin atasaye a garin Agadez.
Sojojin Jamhuriyar Nijar yayin atasaye a garin Agadez. 435th Air Expeditionary Wing Pub - Staff Sgt. Devin Boyer
Talla

Kamfanin dillancin labaran Reuters yace wata sanarwar sojin da ake ta yadawa a kafofin sada zumunta ta ce daukar matakin ya zama wajibi domin kare kasar da kuma kaucewa yiwa sojojin ba-za-ta. 

Kungiyar ECOWAS ta dade tana cewa a shirye take ta yi amfani da karfin soji domin mayar da mulkin fararen hula a Nijar muddin sojojin da suka yi juyin mulki suka ki bada kai. 

Shugaban gudanarwar kungiyar Oumar Torey ya shaidawa manema labarai a jiya juma’a cewar babu wani shiri na mamaye Nijar ko kuma abkawa mutanen ta, yayin da ake ci gaba da daukar matakan diflomasiya domin warware matsalar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.