Isa ga babban shafi

Shugaba Bazoum na Nijar ya yi zawarcin masu zuba jari a London

Shugaba Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijar, ya jagoranci taron masu zuba jari a birnin London a lokacin da ya kai ziyara kasar don halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na 3. 

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da mahalarta taron zuba jari a birnin London.
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da mahalarta taron zuba jari a birnin London. © Niger presidency
Talla

A lokacin taron, shugaba Bazoum ya yaba da alakar da ke tsakanin kasarsa da kuma Birtaniya, inda ya ce Nijar a shirye take wajen bai wa masu zuba jari dama don gudanar da harkokin kasuwancinsu. 

Shugaban ya ce akwai bangarori da dama da masu zuba jari za su iya zuba jarisunsu a ciki, irin noma da kiwo da masana’antu da ma’adinai kamar zinari da Uranium da dai sauran su. 

Shugaban na Niger ya ce domin saukaka harkokin kasuwanci da zuba jari, gwamnatinsa ta yi sauye-sauye a bangaren haraji da kuma saukaka hanyoyin zuba jari. 

Taron dai ya samu halartar da dama daga cikin masu zuba jari na Birtaniya, baya ga jami’an gwamnatin Nijar da suka rufa wa shugaba Bazoum baya.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.