Isa ga babban shafi

An kashe mutane 9 a wani harin da aka kai Tillia dake Jamhuriyar Nijar

Mutane 9 ne aka kashe a ranar Laraba a wani harin da ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai suka kai a wani wuri na ‘yan gudun hijirar.Mali a yammacin Nijar da ke kusa da kasar Mali, kamar yadda majiyoyin tsaro na cikin gida suka sanar.

Taswirar Jamhuriyar Nijar
Taswirar Jamhuriyar Nijar © RFI
Talla

A wannan hari,an bayyana cewa mutun daya ne ya jikkata, shida kuma sun bace," a cewar wani zababben yankin. Harin dai ya ritsa da fararen hula a yankin Tillia, jami'in yankin, ya na main cewa an kai harin ne da yammacin a wani sansanin 'yan gudun hijirar Mali kusa da wani yanki mai nisan kilomita 65 daga arewa maso yammacin Tillia, a yankin Tahoua mai iyaka da kasar  ta Mali.

'Yan ta'addar dauke da muggan makamai" sun zo ne a kan babura guda goma sha biyu, tare da kutsa kai cikin sansanin suka kuma "bude wuta" kafin su gudu zuwa Mali.

Tahoua da Tillabéri  sun kasance  a yankin kan iyakoki uku tsakanin Burkina Faso, Nijar da Mali ,yankuna biyu ne masu girman gaske da ake fama da  rashin kwanciyar hankali, tun a shekara ta 2017 suka fuskanci ayyukan kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS.

A wannan yankin na Tillia ne aka kashe fararen hula 141 a ranar 21 ga Maris, 2021,biyo bayan wani kazamin hari da ake zargin mayakan jihadi ne kan yankunan Bakorat, Intezayane, Woursanat da wasu sansanoni da dama.

A watan Nuwamba 2021, fararen hula 25 ne aka kashe a wani hari da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai a sansanin Bakorat.

A watan Mayu na  shekarar 2022, an kashe sojojin Nijar 16 a wani harin kwantan bauna da wasu ‘yan bindiga suka kai musu a yankin.

Shekara guda da ta wuce, Tillabéri da Tahoua na da 'yan gudun hijirar Mali 61,042 da suka tsere daga arewacin Mali a shekarar 2012, wadanda suka fada karkashin ikon kungiyoyin masu jihadi a cewar Majalisar Dimkin Duniya.

A watan Afrilun 2022, dubban sauran 'yan kasar Mali da 'yan Nijar mazauna Mali sun zauna a wadannan yankuna bayan da suka tsere daga wani kazamin fada a arewacin Mali tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.