Isa ga babban shafi

Algeria ta tiso keyar 'yan ci-ranin Nijar dubu 800 zuwa iyakar Agadez

Mahukuntan Algeria sun tisa keyar 'yan ci-ranin Nijar fiye da 800 zuwa gida wadanda suka shiga kasar ta barauniyar hanya daga iyakarta da garin Agadez.

Tun daga shekarar 2014 Algeria ta fara tiso keyar bakin hauren Nijar zuwa gida.
Tun daga shekarar 2014 Algeria ta fara tiso keyar bakin hauren Nijar zuwa gida. AFP - FATHI NASRI
Talla

Ofishin magajin garin Agadez ya tabbatar da karbar ‘yan ci-rani 847 a jiya alhamis daga mahukuntan na Algeria.

Bayanan da ofishin fitar ya ce cikin ‘yan gudun hijirar da ya karba har da mata 40 da kuma kananan yara 74 ta yadda tuni ma’aikatar kula da kananan yara ta fara basu kulawa.

Wasu bayanai daga majiyoyin agaji sun ce jami’an Algeria sun fara aikin tiso keyar ‘yan gudun hijirar fiye 800 har zuwa kan iyakar garin na Agadez tun a farkon makon nan gabanin kammala tattara su a jiya alhamis.

Majiyar ta ce tuni ‘yan gudun hijirar suka fara samun kulawar gaggawa daga kungiyoyin agaji ta hanyar duba lafiyarsu da kuma wadata su da abinci gabanin rarrabasu zuwa yankunan da suka fito.

Tun daga shekarar 2014 Algeria ke tiso keyar dubban ‘yan Nijar da ke shiga kasar ko dai ci rani ko kuma a kokarin tsallakawa Turai don samun ingantacciyar rayuwa.

Ko a shekarar 2020 sai da Algeria ta tiso keyar ‘yan Nijar dubu 23 da 171 baya ga wasu dubu 27 da 208 a 2021 yayinda daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar nan kasar ta tiso keyar ‘yan ciranin Nijar dubu 14 da 196.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.