Isa ga babban shafi

Shugaban Nijar ya kaddamar da wani shirin samar da abinci a kasar

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bayyana shirin da ya kaddamar na bunkasa noma da samar da abinci da ake kira ‘3N Initiative’ wanda za a kwashe shekaru 4 anayi a fadin kasar.

Shugaban  Nijar Bazoum Mohammed a Kigali
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed a Kigali © Niger Presidency
Talla

Yayin da yake jawabi wajen taron bunkasa noma a nahiyar Afirka da ke gudana a Kigali, Bazoum ya ce shirin ya kunshi bunkasa noman rani, samar da makamashin da manoma za su yi amfani da shi tare da kayan aikin noma da kayan aikin da ake bukata, sai kuma samar da wuraren tattara amfanin gona a yankunan karkara da samar da wuraren ajiya tare da hanyar kai su masana’antu.

Shugaban ya kuma bayyana shirin samar da kasuwannin amfanin gona wanda zai saukaka wa manoma da kamfanonin da ke bukatar amfanin gonar ta inda za su rika hulda a saukake.

Bazoum ya bayyana fatan ganin wannan shiri ya taimaka wajen inganta noma a cikin kasar, wadda akasarin jama’ar ta manoma ne da ke aikin samar da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.