Isa ga babban shafi

Jami'an tsaron Nijar sun kashe 'yan ta'adda 50

Gwamnatin Nijar ta ce 'yan ta’adda dauke da makamai sun kai hari akan jami’an tsaron kasar da ke aiki akan iyakar Burkina Faso, inda suka kashe jandarmeri guda 8 da kuma raunata wasu 33, yayin da jami'an tsaron suka kashe 50 daga cikin 'yan ta'addar.

Wasu daga cikin jami'an tsaron Nijar
Wasu daga cikin jami'an tsaron Nijar U.S. Africa Command - Richard Bumgardner
Talla

Wata sanarwar da Ma’aikatar Tsaron kasar ta sanar ta ce 'yan ta‘addar haye akan babura da motoci sun kai hari akan jami’an tsaron da ke Waraou a kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 5.30 na safiyar ranar Talata, lokacin da Jandarmerin ke gudanar da aiki a wurin.

Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun kashe akalla mutane 50 daga cikin 'yan ta’addar, yayin da su kuma suka jikkata jami’an tsaron guda 6 bayan 8 da suka rasa rayukansu.

Gwamnati ta ce rawar da Jandarmerin suka taka tare da taimakon da suka samu daga wasu abokan aikinsu na kasa da na kasashen duniya ta kasa da sama ya taimaka musu wajen samun nasara.

Sanarwar ta ce rundunar Jandermerin ta yi asarar motocinsu guda 5 tare da babbar mota guda, yayin da ake suke ci gaba da sintiri a yankin yanzu haka.

Garin Waraou na yankin Tillaberi mai fama da tashin hankalin wanda ke kusa da iyakar Mali da burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.