Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta rasa sojojinta 5 a yankin Tillaberi

Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta ce fashewar wani bam ya kashe sojojin kasar biyar a kudu maso yammacin kasar.

Wata mota dauke da jami'an zaben Jamhuriyar Nijar da ta taka nakiya a yankin Tillaberi a shekarar 2021.
Wata mota dauke da jami'an zaben Jamhuriyar Nijar da ta taka nakiya a yankin Tillaberi a shekarar 2021. RFI Hausa/ Salisu Issa
Talla

Sanarwar ta ce, dakarun da suka rasa rayukansu na tsaka da aikin sintiri ne a ranar Larabar da ta gabata a gundumar Gotheye da ke yankin Tillaberi, da yayi iyaka da Burkina Faso da kuma Mali.

Yammacin Nijar ya kwashe shekaru da dama yana fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, duk kuwa da kokarin da dakarun kasa da kasa da aka tura yankin Sahel ke yi domin yakar su.

Nijar, kasa mafi talauci a duniya bisa kididdigar ci gaban bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, na fama da matsalar hare-haren kungiyoyi irin su Daular ISGS a yammacinta, da Boko Haram da kuma ISWAP a kudu maso gabas, kusa da kan iyaka da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.