Isa ga babban shafi
NIJAR-TATTALIN ARZIKI

Nijar na yunkurin bunkasa noma domin ciyar da kan ta - Bazoum

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sha alwashin bunkasa harkokin noma da kiwo da zummar samar da abincin da zai wadata jama’ar cikin kasar da kuma wadanda ke kasashen makota.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed © Niger Presidency
Talla

Shugaban kasa Bazoum Mohammed ya bayyana haka lokacin da yake jawabi wajen taron bikin makon manoma dake gudana a garin Margou ta Jihar Dosso, wanda ya samu halartar manoma da makiyaya daga sassan kasar.

Bazoum na sauraron bayani daga wani kwararre akan hanyar noma
Bazoum na sauraron bayani daga wani kwararre akan hanyar noma © Niger Presidency

Bazoum ya bayyana cewar wani binciken masana da aka gudanar bisa tsari ya nuna cewar ‘Yankin kudancin Nijar daga Dogon Dutse zuwa Gaya da Boboye da Filinge da Margu na da eka miliyan 2 da za’a iya noman rani da damina saboda ruwan da ake da shi kwance a karkahsin kasa da yawan sa ya kai gangan biliyan 600.

Shugaban kasar yace idan gwamnati ta taimakawa manoma da makiyaya da kudin tallafi da kuma tsarin da zasu ci moriyar ruwan, Nijar zata iya ciyar da jama’ar ta da kuma ’yankin Afirka da Yamma.

Shugaba Bazoum na duba kayan aikin gona a Margou
Shugaba Bazoum na duba kayan aikin gona a Margou © Niger Presidency

Saboda haka Bazoum yace gwamnati zata tsaya da kafafun ta wajen ganin ta taimakawa manoman da makiyaya samun tallafin da suke bukata wajen bunkasa sana’ar su wadda zata kaiga daga darajar Jamhuriyar Nijar a idan duniya.

Shugaban yace duk wanda yayi niyar shiga aikin noman na zamani za’a taimaka masa wajen bashi jari ba wai daga bangaren banki kawai ba, har ma da taimakon da gwamnati zata bayar.

Shugaba Bazoum na sauraron mata manoma
Shugaba Bazoum na sauraron mata manoma © Niger Presidency

Bazoum yace asusu guda 3 da gwamnatin Nijar ta bullo da su domin inganta harkar noma da kiwo suna nan, kuma za suyi tattalin su da kuma shiga duniya domin samo karin kudade daga abokan huldar su domin ganin manoma da makiyaya da yawa sun ci moriyar shirin.

Shugaban ya bayyana cewar lalle daminar bana ta zo da matsala saboda katsewar ruwan sama tun daga watan Agusta, abinda ya haifar da karancin abinci, kuma yace wannan ya sa ya tura ministocin sa cikin kasa domin tattara bayanai akan halin da ake ciki.

Jami'an diflomaisyar da suka halarci bikin
Jami'an diflomaisyar da suka halarci bikin © Niger Presidency

Bazoum yace sakamakon da aka gabatar masa ya nuna cewar an samu karancin abinci da yanayi mara kyau, wanda ya bayyana cewar akalla mutane miliyan 8 za suyi fama da karancin abinci, kuma a cikin su, miliyan 2 na neman tallafi a gaggauce.

Shugaban yace gwamnati tayi alkawarin wajen aiwatar da shirin gaggauwa domin taimaka musu ta hanyoyi biyu, da matakin gaggawa da kuma na dogon lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.