Isa ga babban shafi
Nijar-Ambaliyar Ruwa

Mutane 66 sun mutu a sanadiyar ambaliyar ruwa a Nijar

Alkaluma na baya-bayan nan da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka fitar, na nuni da cewa an samu asarar rayukan mutane 66 sakamakon ambaliyar ruwa a sassa daban daban na kasar a daminar bana.

Ambaliyar ruwan ta rusa dubban gidaje a Nijar
Ambaliyar ruwan ta rusa dubban gidaje a Nijar REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ministan Ayyukan Jinkai na kasar Lawan Magaji, ya sanar da taron majalisar ministoci da aka gudanar karshen makon jiya cewa, sama da mutane dubu 151 ne ambaliyar ta bana ta shafa a yankuna daban-daban na kasar.

A cewar ministan, wannan ambaliya ta yi sanadiyyar rushewar gidaje akalla dubu 10 da 409 kafin ranar 1 ga wannan wata na Satumba, yayin da daruruwan dabbobi suka mutu.

Ambaliyar ta bana ta kuma yi sanadiyyar rushewar gidaje, makarantun boko, riyoji da famfunan burtsatse, msallatai, hanyoyin mota da dai sauransu.

Ministan Ayyukan Jinkai Lawan Magaji, ya ce yanzu haka akwai mutane dubu 9 da 867 da ke cikin yanayi na bukatar taimako, to sai dai tuni gwamnati da kuma kungiyoyin agaji da suka hada da UNICEF, Red Cross, Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma hukumar kula da ‘yan ci-rani OIM suka fara daukar matakan tallafa wa jama’a a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.