Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Sani Ibrahim dan farar hula a Nijar game da nasarar Bazoum a zaben shugaban kasa

Wallafawa ranar:

Tsohon Ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi zagaye na biyu sakamakon nasarar da ya samu da kuri’u kashi 55.75 sabanin na abokin karawar sa kuma tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane wanda ya samu kashi 44.25.Shugaban hukumar zabe Issaka Souna ya gabatar da sakamakon, yayin da ya bayyana cewar sakamakon zai tabbata ne lokacin da kotun fasalta kundin tsarin mulki ta tabbatar da shi. Sai dai tuni bangarorin Adawa na kasar suka yi watsi da sakamakon zaben ciki har da Mahamane Ousmane da ya kara da Bazoum a zaben.Dangane da wannan Salisu Isa ya tattauna da Sani Ibrahim wani dan farar hula mai sharhi kan al'amuran siyasar kasar ga kuma yadda hirarsu ta kasance.

Bazoum Muhammad dan takarar shugaban kasar Nijar da hukumar zabe ta bayyana a wanda ya lashe.
Bazoum Muhammad dan takarar shugaban kasar Nijar da hukumar zabe ta bayyana a wanda ya lashe. Mohamed Bazoum
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.