Isa ga babban shafi
Nijar-Faransa

IS ta dauki alhakin kisan Faransawa 6 a Jamhuriyar Nijar

Kungiyar IS ta ce wasu magoya bayan ta ne suka kai kazamin hari kan ma’aikatan agajin Faransa 6 da 'yan rakiyarsu a Jamhuriyar Nijar abinda ya yi sanadiyar hallaka su a gandun dajin da ke dauke da rakuman daji a watan Agusta.

Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mahamadou Issoufou da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mahamadou Issoufou da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kisan da aka yi a ranar 9 ga watan Agusta ne a shafin ta na intanet, inda ta ce wata kungiyar da ke alaka da ita ce ta aikata kisan.

Kungiyar ta danganta kisan da aka yi a yankin Koure da ke kudu maso yammacin birnin Yamai ga kungiyar ISWAP da ke Yankin Afirka ta Yamma.

Kazamin harin ya yi sanadiyar kashe ma’aikatan agajin Faransa guda 6 da direban su dan Nijar da kuma jagoran su.

Su dai wadannan 'yan kasar Faransa da direban su na aiki ne da kamfanin agajin Faransa da ake kira ACTED lokacin da suka ziyarci gandun dajin da ke janyo hankalin baki 'yan kasashen waje.

Faransa da wasu kasashen ketare sun gargadi 'yan kasashen su da su kaucewa tafiya wasu sassan Nijar saboda mayakan boko haram da na ISWAP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.