Isa ga babban shafi
Nijar

Ranar karshe a yakin neman zaben Nijar

A yau juma’a ake kawo karshen yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisar dokoki da za a yi jibi lahadi a jamhuriyar Nijar.Shugaban kasar mai-ci kuma dan takarar a zaben na jibi lahadi Alhaji Issoufou Mahamadou, ya ce ba ya da wata fargaba, zai iya lashe wannan zabe tun a zagayen farko. 

Yan takara a zaben Jamhuriyar Nijar
Yan takara a zaben Jamhuriyar Nijar
Talla

Shugaban wanda ya gudanar da taron gangaminsa na karshe marecen jiya a birnin Yamai, ya ce zai yi nasara ne sakamakon irin ayyuka na ci gaban kasa da ya aiwatar a cikin shekaru biyar da suka gabata.
To sai dai abokannin hamayyarsa na siyasa sun ce ba ta yadda Issoufou Mahamadou zai yi nasara a zagayen farko na wannan zabe.

 Yanzu haka dai akwai ‘yan kallo daga cikin da kuma wajen kasar wadanda hukumar zabe ta bai wa izini sa-ido kan yadda zabe na jibi zai gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.