Isa ga babban shafi
Niger

Dalilan hukumomin Nijar kan halartar gangamin Faransa

Tun bayan da shugaban kasar Niger Mouhamadou Issifou ya je Faransa, don jajantawa ‘yan kasar kan harin da aka kai wa mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo, ‘yan kasar ke ci gaba da bayyana takaici kan lamarin.

Shugaban Nijar Issifou Mahamadou da takwaransa na Faransa Francois Hollande a Paris.
Shugaban Nijar Issifou Mahamadou da takwaransa na Faransa Francois Hollande a Paris. AFP/Dominique Faget
Talla

Sai dai ministan harkokin wajen kasar Bazoum Mohamed ya ce shugaban kasar Issifou ya halarci taron gangamin ne domin kasantuwar Faransa kasar da ke taimaka wa Niger domin tabbatar da tsaro a cikin da kuma kan iyakokinta.

Har ila yau Bazoum ya ci gaba da cewa Nijar kasa ce da ke da milyoyin musulmi, kuma kasar ta yi Allawadai da zanen batanci da jaridar Charlie Hebdo ta yi domin cin zarafin addinin musulunci.

Bayan da shugaban Issifou Mahamadou ya halarci wannan taro da shugabannin kasashen duniya fiye da 40 suka gudanar a birnin Paris bayan kai wancan hari, al’ummar Nijar da dama ne suka bayyana takaicinsu dangane da haka, inda wasu ke zargin cewa shugaban na goyon bayan abin da mujallar ta Charlie Hebdo ta yi ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.