Isa ga babban shafi

'Yan sanda sun bada umarnin janye jami'an tsaron Yahya Bello da EFCC ke nema

Najeriya – Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya Kayode Egbetekun ya bada umarnin janye daukacin jami'an 'yan sandan da ke kula da lafiyar tsohon gwamnan Kogi, Yahya Bello wanda EFCC take nema ruwa a jallo.

Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya Olukayode Adeolu Egbetokun
Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya Olukayode Adeolu Egbetokun © Nigeria Police
Talla

Egbetekun ya bukaci mataimakin sa dake kula da shiyar Kogi da ya tabbatar da aiwatar da umarnin wajen janye daukacin 'yan sandan dake aiki da tsohon gwamnan.

Wannan umarni ya biyo bayan shelar da EFCC tayi na neman tsohon gwamnan wanda tace ya subuce mata tun ranar laraba, lokacin da tayi kwantar bauna a kofar gidan sa.

A ranar laraba, jami'an EFCC sun tare hanyoyin shiga gidan Bello dake Abuja bayan sun yi zargin cewar yaki amsa gayyatar su domin gabatar da bayanai a kan bacewar wasu kudaden jama'ar jihar Kogi da yawan su ya zarce naira biliyan 80.

Rahotanni sun ce, a daidai lokacin da jami'an EFCC ke dakon fitowar tsohon gwamnan domin yin ram da shi, sai sabon gwamnan Kogi Usman Ododo ya ziyarci gidan inda ya dauke shi.

Bayanai sun ce fitowar Ododo daga gidan ya haifar da harbe harbe, lokacin da jami'an tsaron su kayi zargin cewar ya sulale da wanda suke nema, abinda ya sa hukumar EFCC shelar neman sa ruwa a jallo.

Ministan shari'ar Najeriya Lateef Fagbemi ya fitar da sanarwar gargadi ga jami'an dake zagon kasa wajen hana hukumomin tsaro gudanar da ayyukan su, bayan sulalewar Bello da taimakon gwamnan Kogi Ododo.

Tuni hukumar shigi da fice a Najeriya ta sanar da jami'an ta a tashoshin fita kasar cewar kada su kuskura su bar tsohon gwamnan ya tsallaka iyaka, tare da gabatar da lambar fasfo din sa.

Sai dai gwamnatin Kogi ta musanta cewar gwamnan Ododo ya taimaki Yahya Bello kaucewa hukumar EFCC da take neman sa.

Kwamishinan yada labaran jihar, Kingsley Fanwo ya bayyana haka, yayin da yake watsi da zargin da EFCC ta yiwa gwamnan na hana su gudanar da aikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.