Isa ga babban shafi

Sojoji sun kubutar da karin dalibar Chibok bayan shekaru 10

Bayan cika shekaru goma da satar dalibai mata a makarantar sakandiren Chibok da ke arewa maso gabashin Najeriya, Dakarun Operation Hadin Kai, sun kwato guda daga cikin sauran matan da har yanzu ke hannun mayakan Boko Haram din da suka yi garkuwa da su.

Lydia kenan, lokacin da sojoji suka kubutar da ita daga hannun Boko Haram.
Lydia kenan, lokacin da sojoji suka kubutar da ita daga hannun Boko Haram. © dailytrust
Talla

Bayanai sun ce sojojin sun kubutar da Lydia tare da yaranta guda uku, inda kuma take dauke da juna biyu na tsawon watanni biyar.

Yakubu Nkeki shine shugaban kungiyar iyayen ‘yan matan Chibok din da aka sace, ya ce tuni suka samu labarin kubutar da Lydia, kuma a halin yanzu suna jiran kira ne daga gwamnati domin sada ta da iyayen ta.

Ya bayyana cewa, iyayen yarinyar sun bayyana farin cikinsu sosai, bayan da aka kai musu labarin bayyanarta, inda suka ce tuni suka yanke kaunar ganinta, domin sun yi tunanin ta mutu a hannun mayakan.

Shiga alamar sauti, domin sauraron bayanin Yakubu Nkeki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.