Isa ga babban shafi

Ma'aikatan wutar lantarki sun yi Allah wadai da karin kudin wuta a Najeriya

Najeriya – Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki a Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta sake tunani da kuma janye karin kudin wutar da ta fara amfani da shi saboda illar da zai yiwa talaka a cikin kasar.

Wani ma'aikacin wuta a Vietnam
Wani ma'aikacin wuta a Vietnam REUTERS - Nguyen Huy Kham
Talla

Wata wasika da kungiyar ta rubutawa ministan makamashi, ta bayyana matukar damuwarta da karin a kasar da tace an samu tsadar kayayyakin abinci da kuma harkokin yau da kullum.

Wasikar da Sakatare Janar na kungiyar Dominic Igwebike ya rattabawa hannu tace karin kudin zai sa wasu 'yan Najeriya dake da hannu da shuni su koma sayen kayayyakin da ake sarrafawa a kasashen ketare, domin kamfanonin gida ba zasu iya sarrafa masu inganci ba saboda hauhawan farashi.

Igwebike ya kuma ce wannan zai iya sanya wasu kamfanonin da ba zasu iya gogaiya ba rufewa baki daya.

Sakataren ya kuma bayyana cewar karin na iya jefa rayuwar ma'aikatan wutar cikin hadari, sakamakon arangama da fusatattun mutanen da ake zuwa yankewa wutar saboda gaza biyan kudin wutar da suke sha.

Ma'aikatan wutar sun zargi minista da yin gaban kansa wajen karin kudin ba tare da tintibar masu ruwa da tsaki a kan harkar ba, yayin da suka karin ya zarce hankalin jama'a.

Kungiyar ta bayyana karara cewar babu wata gajiya da talakan Najeriya zai ci a kan wannan karin kudin da aka yi.

A kwanakin baya ne gwamnatin Najeriyar ta sanar da karin kudin wutar, yayin da ta bayyana karkasa masu amfani da wutar kashi 4 da kuma abinda kowanne bangare zai dinga biya.

Karin kudin wutar ya gamu da suka daga sasssan jama'a ciki harda masu kanana da manyan masana'antu wadanda suka ce matakin ka iya sanya wasu daga cikin su daina aiki baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.