Isa ga babban shafi

EFCC a gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan Godwin Emefiele

Hukumar yaki da cin hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC, ta gabatar wa babbar kotun jihar Legas sabbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.

Tsohon gwamnan bankin Najeriya Godwin Emefiele.
Tsohon gwamnan bankin Najeriya Godwin Emefiele. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Daga cikin jerin tuhume-tuhumen 26 akwai tafka almundahana wajen fitar da dala biliyan 2 da Emefiele yayi wadanda ya raba wa wasu da ya zaba don taimaka musu wajen samun canjin kudade ba tare da bin ka’ida ba.

Matakin hukumar EFCC ya zo ne a daidai lokacin da fadar gwamnatin Najeriya ta sanar da kammala aikin jami’i na musamman da shugaba Bola Tinubu ya nada wato Jim Obazee, wanda ya gudanar da bincike kan zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.

Obazee wanda Tinubu ya bai wa umarnin fara gudanar da binciken Godwin Emefiele a ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2023, ya gano yadda Emefiele ya bude asusun bankuna 593 a kasashen Amurka da  Birtaniya da kuma China, ba bisa ka’ida ba.

Jami’in ya kuma gano yadda aka yi satar fitar da dala miliyan 6 kwatankwacin naira biliyan 2 da dubu 900 akan canjin kudin da ya kama kan naira 461, a karkashin shugabancin tsohon gwamnan bankin na Najeriya, abinda ya sa Obazee bayar da shawarar hukunta Emefiele da wasu tsafffin jami’ansa 13, cikinsu har da maitaimakansa na shugaban babban bankin, saboda almundahanar da suka tafka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.