Isa ga babban shafi

Rundunar sojin Najeriya ta zargi sarakunan Delta da hannun a kisan sojojinta 17

Babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce sarakunan gargajiyar yankin Okuama da makwabta da ke jihar Delta, sun taka rawa a kisan da aka yiwa sojoji 17 a jihar.

Hotunan sojojin da fusatattun matasa suka kashe a jihar Delta kenan
Hotunan sojojin da fusatattun matasa suka kashe a jihar Delta kenan © DHQ
Talla

A ranar 14 ga watan Maris ne, wasu fusatattun matasa suka kaiwa dakarun bataliya ta 181 harin kwanton bauna, abin da ya haifar da mutuwar sojoji 17 ciki har da masu mukamin Manjo guda biyu da kuma mai mukamin Kyaftin guda daya.

An kaiwa sojojin harin ne lokacin da suke kokarin kwantar da tashin hankalin da ya kunno kai tsakanin kabilar Okuama da kuma Okoloba da ke kudancin Najeriya, a cewar sanarwar da rundunar sojin kasar ta fitar.

Hakan ta sanya rundunar ta ayyana neman wasu sarakuna takwas ruwa a jallo, sakamakon mutuwar manyan sojojin.

Basaraken masarautar Ewu, da ke yankin karamar Ughelli a jihar ta Delta, Clement Ikolo wanda ya kasance cikin wadanda shalkwatar rundunar ke nema ruwa a jallo, yanzu haka yana tsare a hannun a Abuja.

Sai dai sarakunan gargajiyar sun ce basu da hannu a rikicin yankunan da ya kunno da hakan ya yi sanadin mutuwar wadannan sojoji 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.