Isa ga babban shafi

Wasu sabbin gwamnonin Najeriya 13 sun ciyo bashin N226.8bn a watanni shida – DMO

Ofishin kula da basussuka na Najeriya ya ce, Sabbin gwamnoni 16 a kasar sun ciwo wa jihohin su bashi har Naira biliyan 227 a cikin watanni shida kacal da hawansu karagar Mulki.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnonin jihohi yayin taron gudanarwa.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnonin jihohi yayin taron gudanarwa. © Bola Ahmed Tinubu X
Talla

Binciken da jaridar Punch ta gudanar na cewa, gwamnoni 16 sun ƙara yawan basussukan da dama ake bin jihohin su zuwa sama da Naira biliyan 500 sakamakon sabon bashin kusan Naira biliyan 227 da suka ciwo.

Wuraren da gwamnonin suka karbo rancen dai sun hadar da masu ba da bashi na cikin gida da kuma na ketare irin su Bankin Duniya da kuma Asusun ba da lamuni na Duniya IMF.

Jihohi da suka ciyo bashi

Jihohin sun haɗa da Benue da Cross River da Katsina da Neja da Filato da Rivers da Zamfara da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma sun ci bashin sama da Naira biliyan 115 a wurin masu ba da rance na cikin gida, yayin da gwamnonin Ebonyi da Kaduna da Kano da Neja da Filato da Sakkwato da Taraba da kuma Zamfara su ka aro sama da Naira biliyan 111 daga wurin masu ba da lamuni na ketare.

Kamar yadda binciken ya nuna gwamnan jihar Cross River Bassey Otu ne ya fi kowanne cin masu yawan bashin, inda tsakanin watan Yuni zuwa Disambar shekarar 2023 ya aro sama da Naira biliyan 16 a cikin gida sannan ya ci bashin kusan dala miliyan 58 daga waje.

Sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu dai ta yi alkawarin ba za ta rika cin bashin da ba gaira-ba-dalili ba don gudanar da mulkin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.