Isa ga babban shafi

EFCC ta sake bude babin binciken wasu tsofaffin gwamnoni 13

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sake bude wani sabon babin bincike a kan wasu tsoffin gwamnoni da ministoci 13 da take zargi da aikata laifukan almundahana na sama da naira biliyan 853 da miliyan 800.

Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. © EFCC
Talla

Jaridar punch da ta bankado labarin ta ce yanzu haka EFCC na gudanar da bincike a kan tsabar kudi na naira biliyan 81 da miliyan 600 da aka yi sama da fadi da su a ma’aikatar jin kai ta kasar.

Kazalika akwai batun naira biliyan 2 da miliyan 200 da gwamnati ta ware dan siyan makamai da nufin yakar ayyukan ta’addanci da ke addabar kasar, toh amma maimakon haka, aka wawure kudin tare da yin amfani da shi ta hanyar da bata dace ba, kuma wadanda ake zargi sun hada da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, wani shahararren dan wasa marigayi Raymond Dokpesi, sannan tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa akwai kuma tsohon ministan kudi na kasar Bashir Yuguda da dai sauran su.

Betta Edu tubabbiyar ministar jinkai a Najeriya
Betta Edu tubabbiyar ministar jinkai a Najeriya © Daily Trust

Sanarwar EFCC ta kuma lissafa jerin tsoffin ministoticin da take gudanar da bincike a kan su, danage da abin da ya shafi almundahana da dukiyar kasa.

Akwai tsohon gwaman Zamfara Bello Matawalle, da a yanzu ke rike da mukamin ministan harkokin tsaro na kasar karkashin mulkin shugaba Bola Ahmad Tinubu da badakalar naira biliyan 70, sannan tsohon ministan albarkatun kasa kayode Fayemi da naira biliyan 4, akwai kuma tsohon gwamnan Ekiti Ayo Fayose da hukumar ke zargi da yin sama da fadi da naira biliyan 6 da miliyan 900.

Sauran tsoffin gwamnonin da binciken ya shafa sun hada da tsohon gwamnan Nasarawa Abdullahi Adamu da na Kano Rabiu Musa Kwankwaso, sannan tsohon gwamnan jihar Rivers Peter Odili da na Abia Theodore Orji, da na jihar Gombe Danjuma Goje sai Aliyu Wamako na jihar Sokoto, da na Bayelsa Timipre Sylva da kuma Sule Lamido na jihar Jigawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.