Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta fara binciken minista kan zargin badakalar fiye da naira miliyan 500

Gwamnatin Najeriya ta fara binciken badakalar naira miliyan 585.189 da ake zargin ministar jin kai da takaita afkuwar Ibtila’I Beta Edu da aikatawa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © The Guardian
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da wasu kungiyoyin fararen hula kasar suka rika matsawa gwamnatin lamba kan ta gudanar da bincike a kuma hukunta ministar matukar an kama ta da laifi.

Kungiyoyin fararen hular na bukatar gwamnatin Najeriya ta sauke Betta Edu daga mukaminta don samun damar gudanar da ingantaccen bincike ba tare da samun wani katsalandan ba.

Tun farko an zargi Betta Edu da rubutawa Akanta Janar din kasar wata wasika da ke bukatar ta sanya wadannan kudade a cikin asusun wata mata da ba’a san kowacece ba, lamarin da ya tayar da kura.

Sai dai jim kadan bayan fitar labarin, Akanta ganar din kasar ta ce bata saki wadannan kudaden ba, saboda doka sam bata bata damar sanya kudade a asusun wani mutum ba.

Kawo yanzu dai ofishin ministar ya ce ta umarci a biya wadannan kudade ne don baiwa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Lagos, Cross River da Ogun tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.