Isa ga babban shafi

An wuce da basaraken Delta da sojoji ke nema zuwa Abuja bayan miƙa kansa

Sojojin Najeriya sun tisa keyar basaraken nan na masarautar Ewu, da ke jihar Delta, Clement Ikolo zuwa da suka ayyana amatsayin wanda suke nema ruwa ajallo zuwa Abuja.

Sojojin Najeriya yayin sintiri a Kaduna.8/03/24
Sojojin Najeriya yayin sintiri a Kaduna.8/03/24 AP - Sunday Alamba
Talla

Rahotanni sun ce tun a ranar Alhamis ne basaraken ya miƙa kan sa ga ofishin 'yan sandan bayan wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar inda a ciki ta bayyana shi da wasu mutane 7 da take nema ruwa a jallo bisa zarginsu da hannunsu a kisan sojoji 17 a yankin Ughelli na jihar Delta.

Cikin mutanen da take neman har da Farfesa Ekpekpo Arthur, da mahaifiyar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da kai harin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a tun da safiyar Juma'a ne aka miƙa shi ga sojojin.

Sai dai basaraken ya musanta zargin da sojojin suke yi masa yayin wani taron manema labarai kafin daga baya ya miƙa kan nasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.