Isa ga babban shafi

Gobara ta hallaka kananan yara uku a sansanin gudun hijira na Muna a jihar Borno

Bayanai daga Jihar Borno a Najeriya na cewa kananan yara uku sun mutu, yayin da wasu guda 45 suka jikkata sakamakon tashin gobara a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri.

Bayanai sun ce mafi yawan bangare na sansanin ya kone
Bayanai sun ce mafi yawan bangare na sansanin ya kone David Belluz/International Rescue Committee
Talla

Bayan mutanen da suka mutu, wasu karin 783 sun rasa muhallansu sakamakon yadda wutar ta yiwa sansanin barna.

Mahaifin yaran uku da suka mutu Mele Abatcha ya shaidawa manema alabarai cewa kwata-kwata gobarar bata wuce awa guda tana ci ba, amma ta yi wannan irin barna.

Abatcha ya bukaci gwamnati ta yi gaggawar kai musu dauki, la’akari da mummunan yanayin da suke ciki.

Shima a nasa jawabin babban daraktan hukumar bada agaji ta jihar Dr Mohammed Barkindo Saidu ya alakanta faruwar gobarar da cinkoson jama’a a sansanin gudun hijirar.

Ya ce ciyawar da aka yi amfani da ita wajen gina dakunan bukkar da jama’a ke ciki ta baiwa gobarar damar ci cikin hanzari.

Mohammed ya ce bai kamata a ce adadin jama’ar da ke zaune cikin sansanin ya kai haka ba, amma bayanan sirri sun nuna musu cewa wasu daga cikin su ba ‘yan gudun hijira bane, kawai ‘yan gari ne da ke neman abinci na kyauta ne suka tare a sansanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.