Isa ga babban shafi

Sheikh Gumi ya yi tayin shiga tsakani don ceto daliban Kuriga

Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya gamu da kakkausar suka daga daidaikun al’ummar kasar musamman a mabanbantan dandalin sada ciki har da Twitter ko kuma X bayan tayin da ya mika na shiga tsakani don ceto daliban Firamare da Sakandiren garin Kuriga 287 wadanda ‘yan bindiga suka sace a makon jiya.

Shiekh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya.
Shiekh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya. YouTube
Talla

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, ‘yan bindiga suka farwa makarantar Firamare da Sakandiren garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna tare da sace daliban su 287.

Wata sanarwa da ofishin Gumi ya fitar ta bayyana aniyar malamin ta ganin ya taimaka wajen tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriyar da ‘yan bindiga a kokarin kubutar da tarin daliban.

Sanarwar ta Gumi ta ce akwai bukatar gwamnati ta yi amfani da salon da ta yi wajen kubutar da fasinjan jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindiga suka sace cikin watan Maris din 2022.

Ka zalika Sheikh Gumi ya bukaci shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya kaucewa makamancin kuskuren da magabacinsa Muhammadu Buhari ya yi wajen kin amincewa da tattaunawa tsakaninshi da ‘yan bindiga.

A cewar Gumi shawararsa ita ce gwamnatin ta shiga tattaunawa da ‘yan bindiga ba kadai dangane da daliban na Kuriga ba har ma da sauran ilahirin wadanda ke tsare a hannun ‘yan garkuwan.

Sanarwar ta ruwaito Gumi na cewa a shirye ya ke ya siga tattaunawar fahimtar juna don samun damar kubutar da daliban na Kuriga.

Jihar Kaduna na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu satar mutane don kudin fansa wanda a yanzu haka s uke tsare da tarin mutanen da suka sace suke kuma jiran fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.