Isa ga babban shafi

'Yan Najeriya sun kadu da mutuwar Mr. Ibu

‘Yan Najeriya na ci gaba da jimamin rashin shaharerren dan fim din kudancin Najeriya John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu da ya rasu yana da shekaru 62 a Duniya.

Marigayi John Okafor
Marigayi John Okafor © Channels tv
Talla

Tauraruwar Okafor ta fara haskawa ne tun bayan fitowarsa a fim din Mista Ibu kimanin shekaru 20 da suka gabata, inda wannan sunan ne ya zama  sunan da ya fi shahara da shi.

Har zuwa lokacin rasuwarsa yana daya daga cikin zakakuran taurarin da ke taka rawa a fina-finan barkwanci na Nollywood, inda ya fito a fina-finai sama da 200, shahararrun ciki da suka hadar da 9 Wives da kuma Mr Ibu.

A shekarar da ta gabata ne mutane suka fara sanin labarin rashin lafiyarsa wadda a lokacin ta yi kamari, har ta kai ga an yanke kafarsa daya bayan da masoyansa suka hada masa kudi don nema wa kansa lafiya.

Tun daga lokacin ne ‘yan sanda suka cafke dansa mai suna Daniel Okafor da kuma ‘yar rukonsa Jasmine ChIoma bisa zargin su da yin kutse cikin wayarsa tare da kwashe masa kudin da suka kai dala dubu 61.

Kawo yanzu dai ba a ji komai daga bakin ‘yan’yansa ba, amma ana sa ran za a ci gaba da sauraron shara’arsu a ranar 11 ga watan nan na Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.