EFCC ta ce ta bankado naira biliyan 60 a cikin kwanaki 100
Hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta sanar da kwato naira biliyan 60 cikin kasa da kwanaki dari, yayin da ta karbi korafe-korafen cin hanci guda dubu biyar.
Wallafawa ranar:
Yayin da yake jawabin ayyukan da yayi cikin kwanaki 100 da zaman sa shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce cikin korafe-korafe dubu 5 din da aka shigar gaban hukumar ta amince a fara bincike kan sama da dubu 3 yanzu haka daga ciki.
Ya ce bayan naira biliyan 60 din, an kuma kwato wata dala miliyan 10 cikin kasa da watanni hudu da yayi kan kujerar shugabancin hukumar.
Mista Ola, ya ce lamarin cin hanci da rashawa abu ne da ke bukatar hadin kan jama’ar kasar kasancewar EFCC ba zata iya gudanar da wannan aiki ita kadai ba.
Shugaban na EFCC ya yi korafi game da karancin ma’aikata a hukumar, yana mai cewa hukumar da ke sanya idanu kan mutane sama da miliyan 150, tana da ma’aikata 4,800 don haka ba za’a ga tasirin aikin da suke yi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu