Isa ga babban shafi

Takardun bogi aka yi amfani da su wajen cire dala miliyan 6.2 - Boss Mustapha

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha, ya ce takardun da tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele, ya yi ikirarin sun fito ne daga wajen don bada dala miliyan 6 da dubu dari biyu na bogi ne.

Tsohon Sakataren gwammantin Najeriya, Boss Mustapha.
Tsohon Sakataren gwammantin Najeriya, Boss Mustapha. © premiumtimesng
Talla

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban wata kotun Abuja, don bada sheda game da zargin da ake yiwa Emefiele.

Hukumar yaki da rashawa ta kasar EFCC, ta yi zargin cewar Emefiele ya hada kai da wani Odoh Ocheme da yanzu ake nema, wajen fitar da kudin ta hanyar yin amfani da wata wasika da ta fito daga ofishin Boss Mustapha,  mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Janairun 2023.

Toh sai dai lauyan da ke kare Mustapha, Rotimi Jocobs, ya ce wasikar ta bogi ce don kuwa ba daga ofishin shugaban kasa ko sakataren gwamnati ta fito ba.

 

“A tsawon shekarun biyar da wata 7 da nayi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, ban taba cin karo da wadannan takardu da ake ikirarin Buhari ya sanya wa hannu ba."

Boss Mustapha ya kuma karyata amsar wani kaso daga cikin wadancan kudaden da ake zargin, an fitar da su ne don biyar masu sanya ido kan zaben kasar da aka yi a shekarar da ta gabata, ‘yan kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.