Isa ga babban shafi

EFCC a Najeriya ta ayyana neman uwargidan Godwin Emefile ruwa a jallo

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta ayyana neman uwar gidan tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefile ruwa a jallo.

Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. © EFCC
Talla

Hukumar na neman Uwargidan Emefile, da wasu karin manyan kusoshin bankin a zamanin sa da suka hadar da Eric Odoh, da kuma wata fitaciyyar ‘yar kasuwa Anita Omolie da kuma wani rikakken dan chanji Jonathan Omolie.

Sanarwar da hukumar ta fitar tace ana zargin mutanen ne da hada baki da shi Emefile wajen karkatar da wasu makudan kudade mallakin gwamnatin tarayyar kasar lokacin da yake jagorantar bankin.

Bayanai sun ce, uwargidan tsohon gwamnan na CBN ta buya a wani waje da ba’a sani ba a Najeriya, tun bayan da aka kama mai gidanta.

Hukumar ta kuma wallafa hotunan mutanen da take neman din a shafinta na sada zumunta tare da rokon jama’a da su sanar da ita da zarar an gansu.

Wannan dai na zaman wata karin hujja ga hukumar, a ci gaba da shari’ar da ake tafkawa tsakanin ta da Emefile, wanda aka kama tun a ranar da shugaba Tinubu ya sanar da sauke shi daga mukamin sa.

Ana zargin Emefile da cin hanci da rashawa, karkatar da kudaden kasa da halasta kudaden haramun, da kuma sanya son zuciya da sanayya a aikin sa, lamarin da ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin tashin hankali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.