Isa ga babban shafi

An fara zanga-zangar tsadar rayuwa a birnin Legas da ke Najeriya

Wata Kungiyar kare hakkin bil’adama ta fara yin zanga-zangar tsadar rayuwar da ya yiwa mutane katutu a birnin Legas da ke Najeriya.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Najeriya
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Najeriya Reuters
Talla

Wannan dai na zuwa ne duk da gargadin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Adegoke Fayoade ya yi, ta bakin kakin rundunar Benjamin Hundeyin, inda ya ke cewa ba ya son wannan zanga-zangar ta zama sanadiyar shiga hakkin wasu, ta hanyar tare hanyoyi da zai iya jan cunkoson Ababan hawa da kuma kokarin barnatar da dukiyar jama’a ko kuma mallakin gwamnati.

Ita da wannan zanga-zangar kamar ta sharar fage ne ga wadda kungiyar kwadago ta ce za ta fara yi gobe litinin.

Kwamishinan ‘yan sandan ya tabbatarwa da mazauna birnin cewa an baza jami’an tsaro a ko ina don tsare rayukan mutane da dukiyoyin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.