Isa ga babban shafi

Wasu matafiya sunyi zanga zangar jinkirta tashin jirgi a filin jirgin saman Kano

Wasu fasinjojin jirgi da suka fusata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano MAKIA, da ke jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da tsaikon da jirgin Max Air ya yi a yayin da suke shirin zuwa Legas.

rfi
Talla

Jirgin na kamfanin Max Air mai lamba (VM1645) wanda aka shirya zai tashi da farko da karfe 1:00 na rana, sai aka jinkirta lokacin tashisa shi ba tare da an sanar da fasinjojin ba, inda suka zauna na kusan sa'o'i biyar.

Bayanai sun yi nuni da rashin isar da sako daga kamfanin ya kara dagula lamarin, wanda ya haifar da tashin hankali a bangaren sufurin cikin gida.

Malam Abubakar Muhammad wanda yana cikin fasinjojin da abin ya shafa, ya ce ya kamata ya je Legas domin a duba lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.