Isa ga babban shafi

Majalisar dattawa za ta binciki Emefiele da gwamnatin Buhari kan wasu naira tirliyan 30

Majalisar Dattawar Najeriya ta tsaida shawarar gudanar da bincike a kan yadda tshohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da basukan naira tirilliyan 30 da ta karbo daga babban bankin kasar.

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari tare da Godwin Emefiele.
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari tare da Godwin Emefiele. © Sunday Aghaeze>2022/ Arise News
Talla

Gwamnatin Buhari ta yi amfani da tsarin da babban bankin kasar ya kira ‘Ways and Means’ ne, inda ake samar mata da kudaden toshe gibin da aka samu daga a kasasfin kudinta.

Majalisar Dattawar ta ce yadda aka kashe wadannan kudaden da aka karbo daga babban bankin a karkashin jagorancin Emefiele ba bisa ka’ida ba ne ummul’aba’isin matsalar abinci da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Saboda haka ne majalisar ta yanke shawarar kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike a kan yadda gwamnatin Buhari ta kashe naira  tiriliyan 30 din, tana mai  nuni da cewa da gangan aka ki bai wa majalisar dokokin kasar bayani a kan yadda  aka kashe kudaden.

Kwamitin, wanda a Larabar nan za a kadddamar da shi, zai kuma binciki yadda aka bada bashin naira biliyan 10 a karkashin shirin rancen manoma na Anchor Borrowers, da kuma hada-hadar kudaden musanya na kasashen waje da ya kai dala biliyan 2 da miliyan dari 4.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsadar abinci da hauhawar farashin kayayyakin masarufi, faduwar naira da matsalar tsaro ke ci gaba da ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da tawagar tattalin arzikinsa sun sha caccaka bayan da janye tallafin man fetur da ya yi, tare da mayar da tsarin canjin kudaden musanya na bai daya suka jefa al’ummar kasar cikin matsanancin kuncin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.