Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Fasinjoji sun lakada wa ma’aikatan jirgin sama duka a Legas

Fasinjojin jiragen sama na Dana Airline sun lakada wa ma’aikatan kamfanin duka tare da lalata kayan aikinsu, saboda soke tashin jirginsu a filin jirgi na Muratala Mohammed da ke Legas.

Jihar Lagos na daya daga cikin jihohi mafiya hada-hada a filin jiragen sama
Jihar Lagos na daya daga cikin jihohi mafiya hada-hada a filin jiragen sama guardian.ng
Talla

 

A yammacin ranar Litinin ne fusatattun fasinjojin suka dauki matakin sakamakon tsaikon, inda suka lalata wurin da ake tantance fasinjoji kafin su hau jirgi.

Hatsaniyar ta barke ne bayan kamfanin jirgin ya sanar da soke tashin jirage biyu da za su Fatakwal da Owerri daga Legas da karfe 12 na rana, bayan fasinjojin sun shafe sa’o’i suna jira.

Majiyoyi a filin jirgin sun ce wasu fasinjojin sun makale a filin jirgin na sama da sa’o’i 24 bayan da aka dage tashin jirginsu da farko, daga karshe kuma aka soke.

Wani jami’i a filin jirgin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Wasu daga cikin fasinjojin tun jiya (Lahadi) suke jira bayan da aka dage tashin jirginsu.

“An yi musu alkawari cewa jirginsu zai tashi yau (Litinin) amma bayan jinkirin da aka samu na sa’o’i uku, sai aka ce an soke tashin jirgin.”

Hakan ne ya sa fasinjojin kahsewa da kuma lalata na’urorin da kamfanin ke amfani da su a filin jirgin.

Ma’aikatan filin jirgin sun ce a ranar Lahadi, kamfanin jirgin ya yi wa fasinjojin alkawarin cewa jirginsu zai tashi a ranar Litinin da karfe 10 na safe da 12 na rana, saboda matsalar da jirgin  ya samu.

“Abin takaici, sai kusan karfe 6 na yamma kamfanin jirgin saman Dana ya ba da sanarwar soke tashin jiragen biyu ba tare da wani jawabi mai gamsarwa ba, ko zaɓin maido wa jama’a kudadensu.

Dana airline yayi magana

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin a shafinsa na X, hukumar gudanarwar ta nemi afuwar fasinjojin saboda jinkirin da aka samu.

Daga karshe jami’an tsaron jiragen suka shiga lamarin inda aka kira fasinjojin jiragensu suka tashi da misalin karfe 9:00 na dare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.