Isa ga babban shafi

Najeriya: bamu shirya karbar kowane jirgin jigila a matsayin na kasa ba - Keyamo

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeirya Festus Keyamo, ya bayyana cewa babu wani kamfanin jiragen sama na cikin gida da za a ware a matsayin kamfanin jigilar fasinja da kayayyaki na kasar, yana mai cewa yin hakan na iya kasancewa rashin adalci ga sauran kamfanonin jiragen saman dake aiki a cikin gida.

Jirgin saman Air Nigeria a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos, 2014
Jirgin saman Air Nigeria a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos, 2014 © Hansueli Krapf Creative Commons
Talla

Keyamo ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics a ranar Larabar makon da muke ciki.

Ya kuma kara da cewa ma’aikatarsa ​​na kokarin ganin ta samar da jirgin da ya dace na kasa maimakon inganta kamfanin jirgin sama na cikin gida da zai zama mallakin gwmanati ba.

Ministan ya ce, “Zan tura jirgin dakon kaya na kasa guda daya kuma ina aiki a kan daya. Bari in faɗi wannan a bainar jama'a yanzu, babu wani jirgin sama na gida da zai zama jigilar ƙasa, jigilar tuta.

Keyamo ya  ci gaba da cewa a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya gabatar da kamfanin jiragen na Nigeria Air a matsayin wanda zayyi jigila a cikin kasa, lamarin da ya janyo cece-kuce.

An dai ci gaba da cece-kuce a kan kamfanin na Najeriya Air, inda Keyamo ya ce yarjejeniyar ba ta da amfani ga al’ummar kasar.

Majalisar Wakilai ta gayyaci Sirika a shekarar da ta gabata domin amsa tambayoyi game da cece-kucen da ake tafkawa dangane da kamfanin jirgin na Air Nigeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.