Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya za ta fara hukunta jami'an gidajen yarin da ke taimakawa 'yan ta'adda

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara bincike kan wasu daga cikin manyan jami’an kula da gidajen yarin kasar da ake zargi da hada baki da ‘yan ta’adda.

Gidan yarin Kuje da 'yan ta'adda suka kai wa hari a ranar 26 ga watan Yuli, 2022.
Gidan yarin Kuje da 'yan ta'adda suka kai wa hari a ranar 26 ga watan Yuli, 2022. © Afolabi Sotunde, Reuters
Talla

Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya umarci babban kwanturan hukumar kula da gidajen yari na kasar, Haliru Nababa, binciko wasu jami’an hukumar da ake ganin suna hada baki da wasu daurarru wajen taimakawa aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya, ya gano cewa, wasu daga cikin mayakan Boko Haram suna shirya kai hari tare da rarraba kudade da daurarrun da ke tsare.

Hakan ta sanya ministan la’antar wannan danyen aiki da ake zargin wasu jami’an gidajen yari na da hannu a ciki, tare da shan alwashin cewa duk wanda aka samu da laifin, shakka babu zai dandana kudarsa.

Ministan ya ce lokaci yayi da za a fara daukar tsauraran matakai kan masu aikata wannan mummunan aiki, domin ya kasance izina ga ‘yan baya, inda ya ce ya kamata a matsa kaimi wajen inganta sha’anin tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.