Isa ga babban shafi

Boko Haram ta ba mazauna yankunan Borno 8 kwanaki 3 su tashi

’Yan ta’adda da ake zarin mayakan Boko Haram ne sun ba da wa’adin kwanaki uku ga al’ummomin wasu gundumomi takwas a Karamar Hukumar Kaga ta Jihar Borno da su tattare ya nasu ya nasu su bar yankunan ko su yaba wa aya zaki.

Boko Haram
Boko Haram AFP
Talla

Wata majiya a Maiduguri ta ce, jin hakan ke da wuya mazauna yankunan suka tattare suka koma garin Benishiekh, hedkwatar karamar hukumar a ranar Talata.

Mazauna yankunan sun ce ’yan ta’addan sun zarge su da ba tsegunta wa jami’an tsaro kan hare-haren da suka akai a baya-bayan nan da suka halaka da wasu ’yan ta’addan a yankin.

“Mutanenmu suna tserewa daga gidajensu kasancewar ’yan ta’addan ba su da nisa da hanyar Maiduguri zuwa Damaturu saboda zargin mutanen kauyen suna sane da kasancewarsu a yankunan nasu,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa, mutanen yankunan na tsoron ’yan ta’addan za su iya kai farmaki kansu a kowane lokaci shi ya sa suka yanke shawarar tserewa da rayukansu.

A wani labarin kuma, an kashe mutane uku a lokacin da wasu ’yan ta’adda suka kai hari a wani kauye da ke karamar hukumar Konduga a Jihar Borno.

Lamarin da ya afku a yammacin Lahadin da ta gabata ya haifar da fargaba a kauyen da kuma makwabtansa.

Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda  bayan da ’yan ta’adda sun kai hari ga tawagar Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a kan hanyarsu ta komawa Damaturu gaga Maiduguri a yammacin Asabar inda aka kashe wani  dan sanda, wasu bakwai kuma suka samu raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.