Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda 70 sun mutu a wani rikici tsakanin Boko Haram da ISWAP a Najeriya

A Najeriya, kimanin mayaka da kwamandoji 70 ne suka mutu a wani gumurzu da aka yi tsakanin kungiyar ISWAP da Boko Haram a jiya Asabar.

Tutar kungiyaar Boko Haram..
Tutar kungiyaar Boko Haram.. © AFP/STEPHANE YAS
Talla

Gumurzun da aka yi  a Asabar tsakanin Boko Haram da ISWAP, kamaryadda raahotanni suka nuna, ya auku ne a tsibirin Tumbum da ke karamar hukumar Marte ta jihar Borno da misalin karfe 2 na rana.

A cewar wani kwararre a kana bin da ya shafi tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zahazola Makama, kwale-kwale 6 cike da mayaka, Mallakin bangaren Boko Haram karkashin jagorancin Bakura Buduma ne a aka lalata gaba daya.

Majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa rikici tsakanin kungiyoyin ‘yanta’addan da ke adawa da juna ya yi kamari a cikin ‘yan kwanakin nan, sakamakon yadda kari makamai da mayaka ke kwarara daga yankin Sahel don hadewa da kungiyar ISWAP a  Yankin Tafkin Chadi da zummar ci gaba da iko da wurin.

Majiyoyin sun kara da cewa wannan lamari ne ma ya sa dukkannin kungiyoyin ‘yan ta’addan suka kara azama wajen takura wa al’ummar wannan yankin na Tafkin Chadi, wanda ya tilasta wa dimbim ‘yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar su koma gida, lamarin da ya haddasa  cinkoso a sansanin ‘yan gudun hijira da ke  Damasak, a jihar Bornon Na

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.