'Yan ta'adda sun yi wa tawagar jami'an tsaron gwamnan Yobe kwanton bauna
Wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun yi wa tawagar jami’an tsaron gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni kwanton bauna a wannan Asabar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dan sanda guda tare da jikkata 6.
Wallafawa ranar:
Lamarin ya auku ne a kan babban titin Jakana zuwa Mainok na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya. Sai dai gwamnan ba ya tareda su a lokacin harin.
Tawagar jami’an tsaron sun yi wa gwamnan rakiya ne zuwa bikin yaye daliban jami’ar Maiduguri da ke jihar ta Borno, inda aka karrama mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima da digirin girmamawa.
Kakakin gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Mohammed ya ce su ma ‘yan sandan ba su yi kasa a gwiwa ba a lokacin da suka fada cikin tarkon da ‘yan ta’adan suka dana musu, saboda sun mayar da martani ta wajen bude wuta, amma duk da haka suka rasa mutum guda, wasu 3 suka jikkata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu