Isa ga babban shafi

Harin Boko Haram a ofishin kwastan na Yobe ya yi sanadin mutuwar jamií guda

A Najeriya, Wasu da ake zargi mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari ofishin  hukumar Kwastan da ke garin Geidam a karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in kwastan guda.

Tutar kungiyar  Boko Haram kenan.
Tutar kungiyar Boko Haram kenan. © AFP/STEPHANE YAS
Talla

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa maharan sun kutsa  ofishin na kwastan din ne da ke kan hanyar Maine Soroa  a cikin motoci  kirar Golf da Land Rover da misalin karfe 10 na daren Asabar, kuma suka fara harbin kan- mai- uwa- da- wabi.

Wata majiyar tsaro da ta tabbatar da aukuwar wannan lamari ta ce maharan sun kai wannan harin ne a lokacin da suka tabbata jami’an kwastan din sun tashi aiki.

Ruwan harsashai da ‘yan ta’addan suka yi ta yi ya firguita jami’an, har wasu daga cikinsu suka tsere ta wajen tsallaka taga (window), wasu kuma ta kofar shiga harabar ofishin.

Sai dai rahotaanni sun ce an yi rashin sa’a har sai da wani jami’in kwastan daya ya mutu, sakamakon Harbin sa da aka yi a lokacin da ya ke kokarin tserewa ta Katanga.

Maharan sun  kona wata motar sintiri na kwastan, injin samar da lantarki da ginin ofishin.

Mazauna wannan gari na Geidam sun ce ayyukan mayakan Boko Haram sun karu a wajen garin a cikin ‘yan kwanakin nan, inda suka ce har haraji suke karba a gun manoma da makiyaya, kuma ba wanda ya ke yin wani abu a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.