Isa ga babban shafi

'Yan Boko Haram sun janye tubarsu a Borno

Wani rahoton bincike kan halin da tsaro ke ciki a Najeriya, ya ce hare-haren ‘yan ta’adda na kungiyar Boko Haram sun karu a jihar Borno, lamarin da ya yi sanadin salwantar rayuka mutane sama da 250 cikin wata guda. 

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Wata hukumar tsaro mai zaman kanta Beacon Intel, da ke birnin Abuja ce ta wallafa rahoton da ya bayyana cewar a cikin watan Agustan da ya gabata kadai, mutane kusan 300 ‘yan ta’adda suka kashe ya yin hare-haren da suka kai a sassan jihar Borno. 

Cikin rahoton, jagoran hukumar tsaron Dakta Kabiru Adamu, ya ce al’ummomin yankunan da lamarin ya shafa sun danganta karuwar hare-haren na Boko Haram da tayar da  tuban da wasu tsaffin mayakan kungiyar da dama suka yi, inda suka koma dazuka a wasu daga cikin garuruwan da suka hada da Gwoza da Kukawa da Abadam da Damboa da wasu karin yankunan da ke zagayen tafkin Chadi. 

Daya daga cikin tsaffin ‘yan Boko Haram din da aka bayar da misalin tayar da tubansa Yaga Balu, wanda a baya ya mika kansa ga sojoji a garin Gwoza, ya kuma koma cikin al’umma, amma daga bisani ya sake komawa dajin Sambisa, bayan tserewa da wata bindiga da kuma babur. 

Wasu majiyoyi sun ce Balu ne ya jagoranci kai hare-hare da dama a baya bayan nan da suka kashe fiye da mutane 30 cikinsu  har da jami’na tsaro biyu, tare da jikkata wasu da dama. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.