Isa ga babban shafi

Hare-haren Boko Haram na kara tsananta a Arewa maso Gabashin Najeriya

Hare-haren da bangarorin mayakan Boko Haram ke kai wa a sassan jihar Borno wanda ya tsananta a ‘yan kwanakin nan ya tada hankulan al’umma ganin yadda matsalar tsaron ke samun koma baya duk da nasarorin da hukumomi ke ikirarin samu kan mayakan.

Hare-haren mayakan na kara haifar da fargaba a zukatan mazauna yankin.
Hare-haren mayakan na kara haifar da fargaba a zukatan mazauna yankin. AFP - HO
Talla

Ana zargin tsoffin mayakan Boko Haram da su ka tuba aka mu su afuwa da sake komawa dajin su na kitsa kai irin wadannan hare-hare kan al’umma. 

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Bilyaminu Yusuf.

A watan Agusta ne, kwamandan kungiyar Boko Haram da ya haddasa rikicin kabilanci tsakanin mambobin kungiyar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mayaka 82, ya mika kansa ga sojoji.

Amir Bukkwaram ya mikawa sojoji kansa da iyalinsa da mayakansa da dabbobin da kuma makamansu, inda aka mika shi sashi na uku na rundunar Operation Hadin kai da ke garin Monguno a jihar Borno.

Kwamandojin kungiyar Boko Haram 4 da mayakansu 13 da kuma iyayansu 45 ne, suka mika kansu da makamansu ga rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ta’addanci ta MNJTF a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi, a watan Agusta kadai.

Haka nan a ranar 15 ga watan, kwamandoji biyu da mayakansu 4 da kuma iyalansu 24 suka mika kansu da makamai da kuma kudi ga sansanin sojojin rundunar da ke yankin Baga, a wani mataki na amsa kiran da sojojojin su ka yi wa mayakan Boko Haram na su rungumi zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.