Isa ga babban shafi
Najeriya

Mazauna Yankin Tafkin Chadi dubu 30 sun bar muhallansu - MDD

Babban jami’in majalisar dinkin duniya mai lura da ayyukan baiwa ‘yan gudun hijira agaji, Edward Kallon, ya ce sama da mazauna yankin Tafkin Chadi dubu 30 sun tsere daga muhallansu.

Babban jami’in majalisar dinkin duniya mai lura da ayyukan baiwa ‘yan gudun hijira agaji a Najeriya, Edward Kallon, yayin kaddamar da shirin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na shekarar 2018.
Babban jami’in majalisar dinkin duniya mai lura da ayyukan baiwa ‘yan gudun hijira agaji a Najeriya, Edward Kallon, yayin kaddamar da shirin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na shekarar 2018. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mista Kallon ya bayyana sabbin alakaluman ne yayin ziyarar da ya kai garin Mongunu a jihar Borno ranar Laraba, inda ya danganta karuwar wadanda ke rasa muhallan na su da fargabar fuskantar hare-haren da mayakan Boko Haram suke kaiwa wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar jami’in na Majalisar dinkin duniya, yunkurin kai hari garin Monguno da mayakan Boko Haram suka yi a ranar 28 ga watan Disamba, wanda sojin Najeriya suka tarwatsa, ya taka rawa wajen kara yawan wadanda ke barin gidajen nasu.

Edward Kallon ya kara da cewa sama da ‘yan gudun hijira dubu 30,000 sun tsere zuwa Maiduguri mafi akasari daga garin Baga cikin makwanni kalilan, lamarin da ya haddasa cikar sansanonin da ake da su fiye da kima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.