Isa ga babban shafi

Ministan Abuja ya yi barazanar kwace wasu filaye kusan 200

Ministan birnin tarayyar Najeriya Abuja, Nyensom Wike ya dakatar da izinin mallakar filaye da dama da aka baiwa mutane a baya a sassan birnin.

Ministan Abuja NNyensom Wike
Ministan Abuja NNyensom Wike © Nyesome Wike
Talla

Nyensom Wike ya kuma bada umarnin fara gina wasu filaye guda 189 a sassan birnin ko kuma ya kwace hakkin mallakarsu.

Ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ministan, Muhammad Sule ya fitar, ta ce mutanen da umarnin fara ginin ya shafa tuni suka sami sahalewar fara ginin, amma har yanzu basu yi komai a filayen ba.

Sanarwar ta kuma kara da cewa wannan umarni ya zama wajibi, la’akari da irin laifukan da ake aikatawa a irin wadannan filaye da ba a komai da su, da kuma yadda suke lalata tsarin birnin.

Filayen sun hadar da wadanda za a gina gidaje da kuma kamfanoni ko ofisohin kungiyoyi don haka matukar suka zarce wa’adin watanni uku basu fara ginin ba, to babu dalilin da zai hana a kwace a kuma baiwa wadanda suka shirya ginawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.