Najeriya: El-Rufai da Wike na daga cikin tawagar ministocin Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen wasu mutane 28 a matsayin ministocin sa. Jerin sunayen harda tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike. Sunayen na kunshe ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar a wannan Alhamis.
Wallafawa ranar:
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya mikawa majalisar dattijai jerin sunayen ministocin.
Gabatar da sunayen ministocin ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin kasar na kwanaki 60 daga ranar da aka rantsar da sabon shugaban kasa dole ya nada ministoci.
A cikin jerin sunayen ministocin da shugaban majalisar dattawan ya karanta, sun hada da tsofaffin gwamnoni, masana tattalin arziki, masana kiwon lafiya, lauyoyi da abokan Mista Tinubu kai tsaye.
Baya ga Malam El-Rufai da Wike, sauran sunayen sun hada da tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo, Adebayo Adelabu, babban lauya Lateef Fagbemi, masanin tattalin arziki Olawale Edun da kuma mai magana da yawun shugaban kasa Dele Alake, da kuma Barr. Hannatu Musawa wanda ya nada amatsayin mashawarciya ta musamman.
Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar dattawa da ta tantance tare da tabbatar da sunayen ministocin.
Ga jerin sunayen kamar yadda aka karanta:
Abubakar Momoh
Amb. Yusuf Maitama Tugga
Arc. Ahmed Dangiwa
Barr. Hannatu Musawa
Uche Nnsaji
Peter Edu
Sen. David Umahi
Nyesom Wike
Badaru Abubakar
Nasiru El-Rufai
Nkiru Onyejiocha
Olubunmi Ojo
Stella Okotete
Ujo Kennedy Ohaneye
Bello Mohammed
Dele Alake
Lateef Fagbemi
Mohammed Idris
Waheed Adelapo
Emman Suleiman Ibrahim
Farfesa Ali Pate
Farfesa Jeseph Amfani
Abubakar Kyari
John Eno
Sani Abubakar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu