Isa ga babban shafi

Tinubu ya yi kira da akawo karshen juyin mulki a Afirka

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa shugabannin Afirka da su kawo karshen juyin mulki a Nahiyar, wajen maida hankali musamman fuskantar kalubale kamar su annobar COVID-19 da rashin tsaro da kuma sauyin yanayi.

Sabon shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya kenan, Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya kenan, Bola Ahmed Tinubu. © premiumtimes
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa yayin babban taron da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta shirya a daidai lokacin da ake gudanar da taron koli na tsakiyar shekara ta kungiyar AU a kasar Kenya.

Mutunta demokradiya

Tinubu, wanda ya yi kira ga shugabannin Afirka da su mutunta dimokuradiyya, bin doka da oda, da tabbatar da zaman lafiya a siyasance, ya kuma bukaci cibiyoyin sojan Afrika da kasashe su amince tare da mutunta bukatar daurewar dimokradiyya.

Shugaban a cikin jawabinsa, wanda Ambasada Adamu Ibrahim Lamuwa, babban sakatare a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ya gabatar, ya ce, abin takaici ne yadda yammacin Afirka, duk da dimbin kayayyakin aiki da hanyoyin inganta dimokaradiyya da shugabanci na gari, ya kau da kai wajen jagorantar sauran yankuna wajen amfani da hanyoyin da ba bisa ka'ida ba don canza gwamnati.

Shugaban ECOWAS

Shugaban Najeriyar wanda kuma shi ne shugabar kungiyar ECOWAS ta shugabannin kasashe da gwamnatocin bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, ya yi gargadin cewa munanan dabi’un da sojoji ke bijire wa fagen siyasa na haifar da barazana ga zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali, tare da janyo fatara, tarwatsa jama’a, da kuma samar da ayyukan yi ga jama’a da kuma rikice-rikice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.